Amnesty International Ta Nuna Damuwa Kan Tsare Matashin Borno, Samaila Ibrahim Kaigama
- Repoter 11
- 27 Jul, 2026
Amnesty International Ta Nuna Damuwa Kan Tsare Matashin Borno, Samaila Ibrahim Kaigama
Kungiyar ta bukaci a sake shi ko kuma a gurfanar da shi a gaban kotu, tare da gudanar da bincike kan zarge-zargen da ya yi.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta bayyana matukar damuwarta kan kama tare da tsare Samaila Ibrahim Kaigama, wani matashin jagoran matasa daga Jihar Borno, da jami'an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) suka yi bayan wata hira da ya bayar a gidan talabijin.
A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar, ta ce an kama Kaigama ne bayan ya yi wasu manyan zarge-zarge dangane da matsalar rashin tsaro da ta dade tana addabar Jihar Borno.
Amnesty International ta ce yadda aka kama Kaigama da kuma irin yanayin da ake tsare da shi ya jawo tambayoyi masu yawa da ya kamata hukumomi su ba da amsa a kansu.
Kungiyar ta bukaci hukumomin Najeriya da su gaggauta sakin Kaigama, ko kuma su ba shi damar ganawa da lauyoyinsa tare da gurfanar da shi a gaban kotu idan akwai wani laifi da ake zarginsa da aikatawa.
Har ila yau, kungiyar ta ce maimakon ci gaba da tsare shi tare da hana shi samun damar ganawa da lauyoyinsa, ya kamata gwamnatin Najeriya ta fi mayar da hankali wajen gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa da adalci kan zarge-zargen da Kaigama ya bayyana a yayin hirarsa ta talabijin.
Leave a Reply
Your email address will not be published. Required fields are marked *







