:
Breaking News

NBA Ta Yi Allah-Wadai da Sace Alkalin Babbar Kotun Kebbi, Ta Bukaci a Gaggauta Ceto Shi

https://ngazargamuexpressnews.com.ng/public/frontend/img/header-adds/adds.jpg

Kungiyar Lauyoyin Nijeriya (Nigerian Bar Association – NBA) ta yi kakkausar suka kan sace Mai Shari'a Faruku Hassan Bunza na Babbar Kotun Jihar Kebbi da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka yi daga gidansa da ke Karamar Hukumar Bunza.


A cikin wata sanarwa da Shugaban Kungiyar, Afam Osigwe (SAN), ya sanya wa hannu, NBA ta bayyana lamarin a matsayin hari kai tsaye kan bangaren shari'a, gudanar da adalci da kuma mulkin doka a Nijeriya.

Kungiyar ta yi kira da a saki Mai Shari'a Bunza ba tare da wani sharadi ba, tana mai cewa hare-haren da ake kai wa jami'an shari'a na ƙara nuna yadda masu aikata laifuka ke ƙara samun karfin guiwa.

NBA ta bayyana damuwarta cewa irin waɗannan hare-hare na iya raunana amincewar jama'a ga tsarin shari'a, tare da yin kira ga hukumomin tsaro da su dauki matakin gaggawa domin ceto alkalin cikin koshin lafiya.

Kira ga Hukumomin Tsaro

Ƙungiyar ta bukaci Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta DSS, Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro (NSA), da sauran hukumomin tsaro da su tura dukkanin ƙarfinsu domin tabbatar da ceto Mai Shari'a Bunza cikin gaggawa.

Haka kuma, ta roki Gwamnatin Jihar Kebbi da ta haɗa kai da hukumomin tsaron tarayya domin tabbatar da an kubutar da shi tare da kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki domin su fuskanci hukunci.

An Nemi Kara Tsaro ga Alkalai

NBA ta kuma yi kira da a karfafa matakan tsaro ga alkalan ƙasar nan baki ɗaya, tana mai jaddada cewa dole ne a kare su yayin da suke gudanar da aikinsu na kundin tsarin mulki ba tare da tsoro ko barazana ba.

Kungiyar ta kuma bayyana alhini tare da yi wa Mai Shari'a Bunza, iyalansa, abokan aikinsa da ma'aikatan shari'ar Jihar Kebbi addu'ar Allah Ya tsare shi, tare da fatan za a sake shi cikin gaggawa.

Yadda Lamarin Ya Faru

Rahotanni sun bayyana cewa da daren ranar Lahadi ne wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka mamaye gidan Mai Shari'a Faruku Hassan Bunza da ke kan titin Zogirma a Ƙaramar Hukumar Bunza, inda suka yi awon gaba da shi.

Wata majiya daga cikin iyalansa ta ce lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan dawowarsa daga Jihar Sokoto, inda maharan suka tafi da shi ba tare da sun cutar da sauran mutanen gidan ko maƙwabta ba.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya ce rundunar ta tura jami'an musamman da na leƙen asiri domin ceto alƙalin, tare da ƙaddamar da samame a dazuka da wuraren da ake zargin maharan na ɓuya.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata ƙungiya da ta fito ta ɗauki alhakin sace Mai Shari'a Faruku Hassan Bunza.

https://ngazargamuexpressnews.com.ng/public/frontend/img/header-adds/adds.jpg

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *