SHAHARARRIYAR 'YAR SIYASA MAI JINƘAN MARAYU TA YOBE, HAJIYA FATIMA UMAR MAIRIGA TA RASU
- Repoter 11
- 26 Jul, 2026
An shiga jimami a Jihar Yobe bayan rasuwar Hajiya Fatima Umar Mairiga, wadda ta kasance Mataimakiyar Shugabar Mata ta Jam'iyyar APC (Deputy Woman Leader) a Jihar Yobe kuma fitacciyar 'yar siyasa da ta shahara wajen taimakon marayu, zawarawa da masu ƙaramin ƙarfi.
Marigayiyar ta yi fice wajen hidimtawa al'umma, inda ta sadaukar da lokacinta da dukiyarta wajen tallafa wa marasa galihu da kuma ƙarfafa haɗin kan mata a harkokin siyasa da ci gaban al'umma.
Rasuwarta ta jefa iyalanta, 'yan siyasa, magoya bayanta da daukacin al'ummar Jihar Yobe cikin alhini, inda aka bayyana ta a matsayin mace mai tausayi, karamci da kishin jama'a.
Gwamnatin Jihar Yobe ta jajanta wa iyalan marigayiyar, Jam'iyyar APC da daukacin al'ummar jihar kan wannan babban rashi. Gwamnatin ta ce rasuwar Hajiya Fatima Umar Mairiga babban gibi ne ga siyasar jihar da kuma ayyukan jin ƙai da take gudanarwa.
An kuma yi kira ga al'umma da su ci gaba da yi mata addu'ar Allah Ya gafarta mata, Ya yalwata mata rahama, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarta, tare da bai wa iyalanta da masoyanta haƙurin jure wannan babban rashi.
Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.
Leave a Reply
Your email address will not be published. Required fields are marked *
Ahmad Garba Bazam
Allah ya gafarta mata







