:
Breaking News

INEC Ta Fara Daukar Ma'aikatan Dindindin, Ta Bude Shafin Daukar Aiki Ga 'Yan Najeriya

https://ngazargamuexpressnews.com.ng/public/frontend/img/header-adds/adds.jpg

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fara daukar sabbin ma'aikatan dindindin tare da bude shafin neman aikin ga 'yan Najeriya masu cancanta. Aikin ya shafi mukamai daban-daban na matakan Grade Level 8, 9, 10 da 12. 


A bangaren Professional Cadre (GL 9, 10 da 12), hukumar na neman ma'aikata a fannoni kamar ICT Officer, Lawyer, Engineer, Quantity Surveyor da Accountant, tare da wasu mukamai na kwararru. Sannan a Grade Level 8, ana neman Administrative Officer II (Registration Area Officer). 

INEC ta bayyana cewa duk wani ɗan Najeriya mace ko namiji mai shekaru 18 zuwa sama, wanda ke da cikakken hankali, bai taba korar sa daga aikin gwamnati saboda rashin gaskiya ba, kuma bai taba samun hukuncin kotu a matsayin mai laifi ba, na iya neman aikin idan ya cika sauran sharudda. Haka kuma, dole ne mai neman aikin ya mallaki takardar digiri da kuma takardar kammala bautar kasa (NYSC Discharge Certificate) ko takardar keɓewa (Exemption) gwargwadon matsayin da ake nema. 

Hukumar ta jaddada cewa cike fom din neman aikin kyauta ne gaba daya, kuma babu wani kudin da ake biya. Ta gargadi masu neman aikin da su guji duk wanda zai bukaci kudi da sunan samar musu da aiki. 

Masu sha'awar neman aikin za su iya shiga shafin hukuma na daukar ma'aikata na INEC ta hanyar:

[INEC Recruitment Portal](https://recruitment.inecnigeria.org

https://ngazargamuexpressnews.com.ng/public/frontend/img/header-adds/adds.jpg

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *