Ministan Ilimin Indiya Ya Yi Murabus Bayan Zanga-zangar Matasa Kan Satar Takardun Jarabawa
- Repoter 11
- 25 Jul, 2026
Ministan Ilimin Indiya, Dharmendra Pradhan, ya sanar da murabus dinsa a ranar Asabar, bayan kwanaki ana gudanar da zanga-zangar matasa a fadin kasar kan zargin satar da sayar da takardun jarabawar shiga manyan makarantun likitanci.
Masu zanga-zangar, karkashin kungiyar matasa mai suna Cockroach Janta Party (CJP), sun bukaci a hukunta masu hannu a badakalar tare da yin gyara mai zurfi ga tsarin jarabawar kasar.
Dubban dalibai da magoya bayansu ne suka mamaye titunan birnin New Delhi da sauran sassan kasar, suna neman a sauke Ministan Ilimi tare da tabbatar da gaskiya da adalci ga daliban da abin ya shafa.
Bayan sanar da murabus dinsa, kungiyar CJP ta bayyana cewa za ta dakatar da zanga-zangar da take yi a fadin kasar nan take, bayan gwamnatin ta amince da wasu daga cikin bukatunta.
Daga cikin bukatun akwai biyan diyya ga iyalan daliban da rahotanni suka ce sun kashe kansu bayan an soke sakamakon jarabawarsu sakamakon zargin magudi. Haka kuma gwamnati ta amince da duba shirin gyaran tsarin jarabawa mai maki biyar da kungiyar ta gabatar, tare da yin zama da shugabannin kungiyar domin tattaunawa.
Wanda ya kafa kungiyar CJP, Abhijeet Dipke, ya bayyana murabus din Ministan a matsayin nasara ga matasa, amma ya ce har yanzu akwai sauran gyare-gyaren da ake bukata.
A bangaren jam'iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) mai mulki, shugaban jam'iyyar na kasa, Nitin Nabin, ya ce matakin da Pradhan ya dauka ya nuna gaskiya da kishin kasa, yana mai jaddada cewa jam'iyyar na goyon bayansa.
A kwanakin baya dai an samu arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro, lamarin da ya kara ruruta fushin matasa tare da jawo karin goyon baya ga yunkurin.
Masana na kallon murabus din a matsayin daya daga cikin kalubalen siyasa mafi girma da gwamnatin Firaminista Narendra Modi ta fuskanta a wa'adinsa na uku, domin ba kasafai gwamnatin ke sauya matsaya sakamakon zanga-zanga ba.
Masu zanga-zangar sun ce tsarin jarabawar kasar ya dade yana fama da matsaloli, yana jefa dalibai cikin matsin lamba da kuma tilasta iyaye kashe makudan kudade wajen shirya 'ya'yansu domin samun gurbin karatu.
Leave a Reply
Your email address will not be published. Required fields are marked *







