Gwamna Buni ya ja hankalin al’ummar masarautar Ngazargamu kan zaman lafiya da haɗin kai
- Repoter 11
- 25 Jul, 2026
Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni CON COMN, ya buƙaci al’ummar masarautar Ngazargamu da su haɗa kai tare da bai wa sabon Sarkin Ngazargamu, Alhaji Mahmud Ibn Mustapha, goyon baya domin samun nasarar mulkinsa mai amfani ga al’umma baki ɗaya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da sabon Sarkin Ngazargamu tare da al’ummarsa suka kai masa ziyara ta godiya.
Ya tunatar da al’umma cewa ba za a samu ci gaba ba sai an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.
“Masarautar Ngazargamu ta shahara wajen harkokin kasuwanci da ilimin addinin Musulunci, don haka nauyin kowa ne ya tabbatar da an kiyaye tare da inganta waɗannan manyan abubuwan alfahari,” in ji Gwamna Buni.
A nasa jawabin, Wazirin Ngazargamu, Alhaji Baba Kankare, wanda ya yi magana a madadin masarautar, ya gode wa Gwamnan bisa amincewa da zaɓin jama’a na sabon sarki.
Ya ce, “Mai girma Gwamna, kun ba mu zaɓinmu da kuma abin da jama’a suka amince da shi. Muna matuƙar godiya gare ku, mun gode ƙwarai.”
Rahoto daga:
Mamman Mohammed,
Daraktan Yaɗa Labarai da Harkokin Jarida na Gwamnan Jihar Yobe.
Leave a Reply
Your email address will not be published. Required fields are marked *







