:
Breaking News

Gwamnatin Jihar Yobe Ta Amince da Kashe Makudan Kuɗaɗe Kimanin Naira Biliyan 73.3 Domin Gudanar da Manyan Ayyuka

https://ngazargamuexpressnews.com.ng/public/frontend/img/header-adds/adds.jpg

Majalisar Zartarwa ta Jihar Yobe (EXCO) ta amince da kashe kimanin Naira biliyan 73.3 domin aiwatar da manyan ayyukan ci gaba da kuma samar da ayyukan jin daɗin al'umma a faɗin jihar.


Taron majalisar, wanda Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya jagoranta, ya amince da ware sama da Naira biliyan 28.531 domin sayo kayayyakin noma da kayan aikin gona a ƙarƙashin shirin bunƙasa noma na shekarar 2026.

Haka kuma, majalisar ta tabbatar da kashe sama da Naira biliyan 4.939 domin gina Tashar Mota ta Zamani da Kasuwar Hatsi a Buni-Yadi, tare da amincewa da kashe Naira biliyan 5.688 domin kammala manyan ayyukan waje da ƙarfafa katangar Tashar Mota ta Zamani da ke Damaturu, wadda ke dab da kammaluwa.

Majalisar ta kuma amince da kashe sama da Naira biliyan 3.945 domin gina sabuwar babbar kasuwa da ƙaramar kasuwa a garin Buni-Gari.

Har ila yau, ta tabbatar da kashe Naira miliyan 652.627 domin sayen kamfanin Fanzar Mixed Farms Ltd, sannan ta amince da kashe Naira biliyan 1.177 domin gina sabon hedikwatar Ma'aikatar Gidaje ta Jihar Yobe.

A bangaren gidaje kuwa, an amince da kashe Naira biliyan 2.248 domin sayen gidaje 208 daga Ma'aikatar Gidaje da Raya Birane ta Tarayya.

Majalisar ta kuma amince da gyara, kawata da inganta manyan zagayowar hanya guda huɗu a birnin Damaturu tare da sanya shingayen kariya, sannan da ƙarin ayyukan inganta Damaturu Mega Shopping Mall, wanda ake ci gaba da ginawa.

Domin ƙarfafa mata masu sana'o'i da dogaro da kai, majalisar ta amince da kashe Naira miliyan 460.828 domin sayen buhunan wake 1,780 masu nauyin kilo 50, waɗanda za a raba wa mata masu ƙananan sana'o'i tare da man girki, murhunan da ba sa hayaki, kayan girki da sauran kayayyakin da tuni aka tanada.

Hakazalika, ta amince da kashe Naira miliyan 364.475 domin sayen injinan niƙa 1,000 na Yamaha GX390, waɗanda za a raba wa al'umma a matsayin tallafin dogaro da kai.

A fannin hanyoyi kuwa, majalisar ta tabbatar da kashe Naira biliyan 23.975 domin manyan ayyukan hanyoyi guda biyu. Wannan ya haɗa da Naira biliyan 21.904 domin gyaran da shimfiɗa kwalta a hanyar Kalallawa–Kaliyari mai tsawon kilomita 45 a ƙananan hukumomin Damaturu da Tarmuwa, da kuma Naira biliyan 2.071 domin gina hanyar Damagum–Gubana mai tsawon kilomita 7, wanda zai cika kilomita 17 na hanyar zuwa garin Gubana.

A ƙarshe, Majalisar Zartarwar ta amince da haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu (PPP) domin mayar da Ofishin Hulɗa na Jihar Yobe da ke Kaduna zuwa otel na zamani ta tsarin Build-Operate-and-Transfer (BOT). A ƙarƙashin wannan tsari, za a ci gaba da amfani da ofishin hulɗar, sannan bayan shekaru goma mallakar dukkan kadarar za ta koma hannun Gwamnatin Jihar Yobe.

https://ngazargamuexpressnews.com.ng/public/frontend/img/header-adds/adds.jpg

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *