:
Breaking News

Jihar Jigawa Ta Kawo Karshen Rikicin Iyaka Tsakaninta da Jamhuriyar Nijar Bayan Shekaru 47

https://ngazargamuexpressnews.com.ng/public/frontend/img/header-adds/adds.jpg

Gwamnatin Jihar Jigawa ta sanar da kawo ƙarshen rikicin iyaka da ya daɗe yana ci tsakanin al'ummar Jobi da ke Najeriya da kuma Kyalli da ke Jamhuriyar Nijar, rikicin da ya shafe kusan shekaru 47 yana ci tare da haddasa mutuwar sama da mutane 1,000.


Rikicin ya samo asali ne tun a shekarar 1979 sakamakon takaddama kan mallakar filayen noma, lamarin da ya rika hana manoma gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali tare da janyo zaman ɗar-ɗar da rashin jituwa tsakanin al'ummomin da ke makwabtaka da juna.

An cimma yarjejeniyar zaman lafiya ne yayin bikin rabon madadin filayen noma ga manoman da rikicin ya shafa. A matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar, gwamnati ta raba filayen noma ga manoma 74 daga ƙauyen Jobi, sannan ta samar da ƙarin filaye ga wasu manoma 30.

Haka kuma, gwamnatin jihar ta amince da mayar da wani sashe na dajin Dan Maka zuwa filayen noma domin biyan diyya ga waɗanda rikicin ya shafa.

Wasu daga cikin mazauna yankin, Musa Ahmad da Salisu Kabir, sun bayyana farin cikinsu kan sasanta rikicin, inda suka ce yanzu za su iya komawa gonakinsu ba tare da fargabar tashin hankali ba.

Sun kuma yi alkawarin ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya tare da maƙwabtansu, tare da mara wa duk wani yunkuri na tabbatar da dorewar zaman lafiya a yankunan iyaka baya.

Kawo ƙarshen wannan rikici, wanda ya kasance ɗaya daga cikin mafi tsawon rikice-rikicen da suka shafi iyaka a yankin, ya nuna muhimmancin tattaunawa, haɗin kai da kuma shiga tsakanin al'umma wajen tabbatar da zaman lafiya, wadatar abinci da kwanciyar hankali a kan iyakokin Najeriya.

A wani ɓangare kuma, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, bisa ƙoƙarinsa na inganta zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al'ummomin da ke yankunan iyakar jihar.

Babban Daraktan Hukumar Kula da Iyakokin Ƙasa ta Najeriya (National Boundary Commission), Surveyor Adamu Adaji, ne ya bayyana hakan yayin bikin ƙaddamar da rabon madadin filayen noma ga al'ummar Jobi. Wakiliyar sa, Daraktar Sashen Iyakokin Ƙasa da Ƙasa, Hajiya Yahanasu Aliyu, ta ce rabon filayen wani muhimmin mataki ne na warware tsohon rikicin filayen noma tsakanin al'ummar Jobi da ke Najeriya da kuma Kyalli da ke Jamhuriyar Nijar.

https://ngazargamuexpressnews.com.ng/public/frontend/img/header-adds/adds.jpg

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *