:
Breaking News

JAMB Ta Fara Rajistar Shiga NCE da Wasu Kwasa-Kwasan ND ba Tare da Rubuta UTME ba

https://ngazargamuexpressnews.com.ng/public/frontend/img/header-adds/adds.jpg

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) ta sanar da fara rajistar masu neman gurbin karatu a NCE da kuma wasu zababbun kwasa-kwasan National Diploma (ND) na fannin noma ba tare da bukatar rubuta Jarabawar UTME ba.


Wannan sabon tsarin ya biyo bayan umarnin Gwamnatin Tarayya na kara yawan masu shiga Kwalejojin Ilimi tare da karfafa gwiwar 'yan Najeriya su zabi fannin noma a matsayin sana'a da hanyar samun ilimi.

Duk da cewa ba za a bukaci masu neman gurbin karatu su rubuta jarabawar UTME ba, JAMB ta bayyana cewa dukkanin guraben karatun za su ci gaba da bi ta tsarin Central Admissions Processing System (CAPS) domin tabbatar da tantancewa, inganta sahihancin bayanai, da kuma kiyaye ingancin tsarin bayar da guraben karatu.

https://ngazargamuexpressnews.com.ng/public/frontend/img/header-adds/adds.jpg

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *